Category Archives: HUDUBAR MALAMAI DA GA MUNBARIN JUMA’A

KUSANTAR ALLAH DA KYAWAWAN AYYUKA.

Bayan Malam ya girmama Allah da kirarimaigirmangaske, ya kuma yi salati ga fiyayyen halittada addu’a ga alayensa da sahabbansa da duk wanda suka biyobayansu da kyautatawa.

Malam ya fara huduba da yi mana nasiha kan cewa muji tsoron Allah, kamar yanda Allah ya fada a wurare masu yawa irin abubuwa da Allah zaiyi wa duk wanda yaji tsoron Allah. Bayan haka Malam ya ci gaba da cewa bayan yin wasilci da tsoron Allah babu abin daya kamata muyi wasiyya da shi kamar yanda al’amarin al’ummar nan ya gabata kancewa bayan wasiyya da jin tsoron Allah da yawan ta tuba gareshi, sai kuma kusan tar Allah da kyawawan Ayyuka. Continue reading →

ILMI AMANA NE.

Wannar huduba tazo daidai lokacin da da yawa cikin daliban manyan makarantu na gaba da sakandare suke rubuta jarrabawa, wassu kuma suna shirin farawa a ‘yan kwanaki kadan masu zuwa, musamman daliban Jami’a Mallakar jihar Gombe wanda suke shirye-shiryen farawa.

Malam yayi amfani da wannar dama yayi kira da babbar murya ga dalibai su dage matuka wajen karatu, da kuma nacewa da addu’a. ya kuma tsawatar kan harkar magudin jarrabawa yana me bayyana munin hakan da haramcinsa a shari’a.
Hudubar ta kunshi muhimman abububuwa da dukkan musulmi zai so ya sauraresu ya kuma yi amfani dasu, musamman su dalibai masu shirin rubuta jarrabawa. Continue reading →

Fitintinun da suke faruwa a garuruwan musulmi a yau

Ya bude hudubar tasa ne da yabo ga Allah da kuma salati da sallama ga Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi.
Sannan ya yi wasici da jin tsoron Allah madaukakin sarki.
Ya kusa cikin hudubar tasa yana mai Magana dangane da fitintinun da suke faruwa a garuruwan musulmi a yau.
Yana mai cewa fitintinu a yau sun kewaye musulmi a garuruwansu ta ko ina, wadda musibar da tafi ko wacce girma da cutarwa a cikin musulmi a yau it ace: musibar sabani da rarrabuwar kai, da kuma yaduwar kiyayya da kin jinin juna kuma duk sabo da kawar rayuwar duniya, wanda basu farga ba har wannan sharri ya zo ya mamayesu ya fantsama a cikinsu, Continue reading →

KYAWAWAN AYYUKA DA KYAWAWAN NIYYOYI

Bayan Malam ya girmama Allah da kirari mai girman gaske, ya kuma yi salati ga fiyayyen halitta da addu’a ga alayensa da sahabbansa da duk wanda suka biyo bayansu da kyautatawa.

‘Yan uwa Musulmi muji tsoron Allah, sannan mu duba ayyukan da muke gabatarwa kawunan mu na ayyuka da niyyoyi da muka kullata a zukatan mu domin Allah Jalla wa’ala ya halitta mu domin yaga wanene yafi kyakkyawan aiki a wannan rayuwa. Ta haka ne kuma Allah bai kyalemu ba sai da ya bayyana mana tafarkin Alhairi da kuma tafarkin sharri, sannan bayan ya bayyana wannan Allah yayi mana muwafaqa da kyawawan ayyuka dukkan wanda ya kullaci wata niyya a cikin zuciyarsa.

Mu sani cewar Allah madaukakin sarki ya shar’anta mana da ayyuka da niyya zasu zama sababin tsiran mutum komai lalacewarsa domin Allah Jalla wa’ala baya kallon surar mutane, baya kallon dukiyoyinsu saidai Allah yana kallon ayyukansu ne da kuma zukatansu. Kuma sakamako Allah yanayi ne daga abin da mutum ya kasance yana aikatawa. Abubuwan da muke gani anan, kamar yanda mutum yayi mu’amala haka Allah zaiyi mu’amala da shi, idan yayi mu’amala da Allah a bias alkhairi to Allah zai yimu’amala da shi a bias alkhairi tun a nan duniya sa’annan kuma idan yakoma ranar Qiyama yacika masa alkhairi. Idan kuma yayi mu’amala da shi ta sharri, to Allah zai mu’amalanceshi da misalin abin da yayi.

Annabi (S. A. W) yace Allah ya rubuta kwawawan ayyuka ya kuma rubuta munanan ayyuka, sannan ya bayyana wannan, duk wanda yayi niyyar aikata kyakkyawa amma bai aikata wannan kyakkyawan aikiba to Allah zai rubuta masa wannan a matsayin kyakkyawan aiki cikakke. Idan yayi niyyar kyakkyawan aiki sannan ya aikata wannan kyakkyawan aiki, to Allah zai rubutashi a matsayin kyakkyawan aiki guda goma har ya rubuntashi zuwa dari shida har zuwa ga ninkin-baninkin abin da Allah ne kawai ya san yawansa. Idan mutum yayi niyyar aikata mummuna sai kuma bai aikata mummunan ba, to Allah zai rubuta wannan rashin aikata mummunan a matsayin kyakkyawan aikine. Idan mutum yayi niyyar aikata mummuna kuma ya aikata, to Allah zai rubuta wannan mummuna a matsayin mummuna guda daya.

Idan mutum ya bada sadaka Allah yana ninka ladan har ya zuwa dari bakwai har ya zuwa ladan da shi kadai yasani. Akwai ayyukan da Allah ne kawai yasan yawan ladansu, kamar Azumi

WANDA YA GABATAR: DR. BASHEER ALIYU OMAR

Girman Annabi (S.A.W)

بسم الله الرحمان الرحيم.
Duk da dai Allah bai bani daman isa masallaci akan lokaci ba, ga dan kadan daga abinda na tsakuro mana…

Na shigo malam yana kan magana akan girmama annabi(صلى الله عليه وسلم‏)‏
Annabi shine fiyayye aduk cikin halittun Allah baki daya, dolene ga duk musulmi yayi koyi dashi acikin duka lamuransa…. Yaci gaba da bayani har ya gangaro kan yahud da nasara, yace bai dace ace musulmi yayi koyi dasu ba ta ko wata hanya, haka kuma bashi yiwuwa mutum ya sosu. Acikin zancensa sai ya kawo fadin Allah(subhanahu wa ta’ala) acikin suratu baqara ayah ta 120
وَلَنْ تَرْضَى عَنْكَ الْيَهُودُ ولَا النَّصَارَى حَتَّى تَتَّبِعَ مِلَّتَهُم قُلْ إِنَّ هُدَى اللَّهِ هُوَ الْهُدَى وَلَئِنِ اتَّبَعْتَ أَهْوَا ءهُمْ بَعْدَ الَّذِي جَاءَكَ مِنَ الْعِلْمِ مَا لَكَ مِنَ اللَّهِ مِنْ وَلِيٍّ وَلَا نَصِيرٍ Continue reading →

GABATARWAR HUDUBAR MALAMAI DAGA MUNBARI

Wannan sahe zai rika kawo muku Hudubar da malamai suke gabatarwa ne daga Masallatai daban-daban. Wannan kuma zai hada har da malamai magabata da hudubobinsu.

Za ka iya aiko muna abin da hudubar masallacinku ta kunsa domin mu wallafa muku. Allah ya sa mu dace.