Kibiyar Tsautasyi (2)

kibiyar tsautsayiCi gaba daga inda muka tsaya a kashi na daya

Hankalin Ladidi ya yi matukar tashi sanadiyar wadannan tambayoyi, domin ta san ko shakka babu wani al’amari mai muni ya faru da kawarta. Amma sai ta yi kamar ba ta fahimci wani abu ne ya faru ba. Kai tsaye ta shawarci Lubabatu da su je wajen malam domin samun amsoshin tambayoyin. Nan take suka sulale daga gidan bukin ba tare da kowa ya sani ba. Continue reading →

Kibiyar Tsautsayi 1

kibiyar tsautsayi

Ba sai an gaya maka ba, yanayin zaman zugum din da ke ci gaba da wanzuwa tsakanin Alhaji Bala da matarsa Ladidi, tare da ’yarsu Zuwaira wadda ke gefe daya tamkar ruwa ya cinye ta ne, zai tabbatar maka da cewar ba lafiya ba!
“Zama hakan fa ba zai kawo wani sauyi daga wannan tsautsayi da ya same mu ba, ta yaya za a ce yarinyar nan na da juna biyu kuma har ya kai watanni biyu ba tare da mun sani ba?’’ Ladidi ce ta fadi hakan a lokacin da Alhaji Bala ya kura mata idanuwa cike da son ya dora alhakin wannan sakacin a kan ta.
Abin da Alhaji Bala bai sani ba shi ne, Continue reading →

Shawarar Dakta Gumi Zuwa Ga Buhari: Magana ɗaya ce ta rosa komai

Shawarar Dakta Gumi Zuwa Ga Buhari: Magana ɗaya ce ta rosa komai

Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai

Janar Muhammadu Buhari, shi ne ɗan takara guda ɗaya tak da za ka samu cewa talakawa ne da kansu suke son sa, kuma suke son ya shugabance su domin su samu mafita daga wahalhalun da suka samu kansu a ciki. Ko shakka babu, Janar Buhari ne kawai ɗan takarar da talakan Najeriya zai iya jefawa ƙuri’arsa ba tare da an ba shi ko sisin kwabo ba. Har ila yau, janar Buhari ne kawai wanda ko ka san kuskurensa, kake tsoron furta shi a gaban al’umma komai kyakkyawar manufar da kake da ita a cikin furta zancen. Wannan kuwa, domin Buhari ne kawai ɗan siyasar da ake iya cewa alhairinsa ya fi sharrinsa yawa kai tsaye. Continue reading →

http://www.tickcounter.com/countdown/2014jun18/Europe+London/040000pm/ADIYA%2520ISLAMIYYA%2520HOLIDAY

Y’AN UWA MU TUNA DA KAUYUKANMU

Mutum da Mutum ƴan uwan juna ne tun azal, ba wai sai an haife su gida ɗaya ba. Kuma ko wane ɗan uwa dole za ka sa me shi yana son ɗan uwansa, a koda yaushe yana kula da shi idan shi ne ke kan gaba, shi kuma wanda ake kan gaban shi yana nuna biyayyarsa ga wanda yake gaba da shi. Idan kuma aka sami akasin haka daga gefe ɗaya, to lalle wanda aka samu giɓi daga gefensa yana da matsala ta jahilci duniyance da addinance ko ƙaramcin wayewa.

Ba lalle ba ne, wanda ya fi girman shekaru shi ne zai taimakawa ƙarami ba, Continue reading →

Allah Ya isarwa Adamu Zango

Ina mamakin mutane irina, masu bala’in kauxi da shiga lamarin da bai shafe su ba. Amma ni dai ina da y’ar dama-dama daga cikinsu, tunda ni ina yi ne da niyyar yin hannunka mai sanda. Shi ya sa ban cika ba wa kaina haushi sosa-sosai ba. Idan ba kauxi da shiga abin da ba’a sa mutum ba, ina ruwanka da yawo kana yaxa labarin cewa Adamu ya yi wa Nafisa Abdullahi (sai watarana) ciki? To yanzu dai ta faru ta qare, don Adamu xin da kansa ya mayar da martani, yana mai cewa bai yafe ba, idan an haxu lafira Allah zai yi muku hisabi.

Idan akwai wani abu da ya kamata a ja hankalin Adamu Zango akai shi ne: Continue reading →

Kaiconka Ali Baba, Malamai Ba abin Wasa Ba Ne

Y’an wasu watanni kad’an da suka shud’e a baya, mai baiwa gwamnan Kano
shawara akan harkar Addini, waton Ali Baba ya yi wasu kalamai masu
cike da cin mutunci da tozarci ga malaman addinin musulunci. Domin
kwatanta malamai da masu shirya fina-finai, kwatance ne mai cike da
zalunci da rashin sanin ya kamata.
A wancan lokacin, Ali Baban ya yi i’kirarin cewa: Continue reading →