Monthly Archives: March, 2013

Mai Gidan Gilas Bai Dace Yayi Wasar Jifa Ba

Da sunan Allah mai rahama mai jinqai

Haqiqa harshe yana tattare da alkhairai da kuma hatsarin gaske da kan shafi rayuwa ta vangarori da dama, tasirinsa wurin qulla sharri ko alkhairi, yana kasancewa abisa tsarin da mai shi ya xora shi akai. Kamar Idan mutum ya zavi harshensa a matsayin wani makami da zai qulla alkhairi da shi, yayi hani da sharri tare da horo da aikata alkhairi, za ka ga cewa a duk lokacin da ya furta magana babu suka ko zagin kowa a ciki sai dai Alkhairi. Za ka samu kowa yana maraba da kalamansa tare da jin daxin zancensa. Za ka ji mutane idan sun buxa baki suna ambaton alkhairi akansa. Continue reading →

Kamanta ‘Yan Fim Da Malaman Addini Da’ki’kanci ne

Da sunan Allah mai rahama mai jin’kai.
A kowace rana ko safiya ta Allah wani sabon al’amari kake jin yana fitowa daga wad’anda ba ka yi tsammani ko zato ba! A rayuwa akwai ban tausayi, idan ka ga mutum da siffar masu ‘kima amma kalamansa su ri’ka kasancewa na mahaukata tuburan. Babu wata hauka da take da ban tausayi a cikin nau’ukan hauka wadda ta kai haukar da mai ita bai yadda shi mahaukaci ba ne. Continue reading →

MANUFOFIN KARA AURE

Kishi wata dabi’a ce da Allah ya halicci mata akanta, Nana A’isha tana cewa : “Ban taba yin wani kishi ba, irin kishin da na yiwa Khadijah, kuma ban taba ganinta ba, saboda yadda na ji Annabi s.a.w yana ambatonta” Bukhari 1388

Kishi mai tsafta, shi ne : kishiya ta yi rige-rige da kishiyarta, wajan kyautatawa mijinsu, akwai hikomi masu dimbin yawa da suka sa shari’ar musulunci ta yi umarni da Karin aure, ga wasu daga ciki: Continue reading →

BABBAR FITINA A RAYUWAR MATASA

BABBAR FITINA A RAYUWAR MATASA ITA CE SHA’AWA.

A wannan zamanin wani muhimmin abu da ya addabi mutane sosai, musamman matasa maza da mata shine SHA’AWA, kusan kullum matasa na fadawa cikin bala’in fasikanci kala-kala a dalilin rashin sanin hanyar kauce wa haka. Idan mutum ya yi duba na tsanaki tareda la’akari da yanayinmu da kuma yanayin zamani zaiga cewar da yawa wasu na fadawa cikin aikata fasiqanci ba cikin son ransu ba, sai don abin ya fi karfinsu. Sau da yawaza ka ga matashi mai hankali mai tarbiyya mai tsoron ALLAH, ya san illar zina, ya san girman zunubinta, amma saboda fitinar sha’awa ya kasa daurewa ya je ya aikata din. Wani haka zai ta aikatawa ya na tuba, da haka har zina ta zame ma sa jiki ya runka ganin ai yin taba komai bane Subhanallah! Continue reading →

MU YAWAITA TUNANIN MAI KATSE JIN DADI (MUTUWA)

Rayuwa mai farko Mai karshe. Yana da kyau mu dinga tuna Mai yanke rayuwa da Jin dadi itace MUTUWA.! Zuwan ta ba sanarwa, kwatsam zata zo ga kowa ko da so, ko da ki haka za’a tafi baa gama shiri da hidimomin mu na rayuwa ba.

A kullum muna sa tufafi mu fita hidimomi, wata rana in kasa tube maka za’a yi don wankan gawa. Muna gyara jiki muyi kwalliya da ado wata rana kasa ce zata ci naman mu a kabari. Muna zama mu shirya gobe da tsare tsaren shekaru don buri muna mantuwa da cewa wata rana sai taron jana’izar mu yazo ba mu gama cika buri ba. Continue reading →

ABUBUWA GUDA GOMA SUNA KARIYA DAGA SHAIDAN

Bawa yana samun kariya daga Shaidan da abubuwa guda goma:

1. Neman tsari da shi kamar yadda Allah ya yi umarni da hakan a al’qur’ani.
2. Karanta kula’uzai guda biyu.
3. Karanta ayatul kursiyyu
4. Karanta suratul bakara.
5. Karanta ayoyi biyun karshe na suratul bakara.
6. Karanta ayoyi uku na farkon suratul Gafir.
7. Karanta Laa’ilaha illallahu wadahu laa shariikalahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa alaa kulli sha’in kadeer, sau dari.
8. Yawan ambaton Allah
9. Yin alwala lokacin sallah.
10. Barin kallo da zancen da ba shi da amfani, da abincin da ya wuce bukata, da barin cakuduwa da mutane, sai gwargwadon bukata.

Daga: Malam Jamilu Zarewa

KWADAITARWA..!!! DON MASU HAWA SOCIAL NETWORKS

Yin COMMENT ko LIKE na POST MAI MA’ANA, na kama da wadannan ababe:
= YA DA ALKHAIRI, dan a duk lokacinda kayi daya daga cikinsu sai Friends dinka sun gani, za kuma a samu wadanda za su karanta su amfana.
= TARAYYA CIKIN LADA, shi da ya yi Post din yana da lada, haka kai da kayi like, share, tag za ka samu ladan wadanda suka amfana a dalilinka.

= KARAWA MAI YI KARFIN GWUIWA, cire ZARGI da TUNANIN cewa Continue reading →