Monthly Archives: October, 2014

Shawarar Dakta Gumi Zuwa Ga Buhari: Magana ɗaya ce ta rosa komai

Shawarar Dakta Gumi Zuwa Ga Buhari: Magana ɗaya ce ta rosa komai

Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai

Janar Muhammadu Buhari, shi ne ɗan takara guda ɗaya tak da za ka samu cewa talakawa ne da kansu suke son sa, kuma suke son ya shugabance su domin su samu mafita daga wahalhalun da suka samu kansu a ciki. Ko shakka babu, Janar Buhari ne kawai ɗan takarar da talakan Najeriya zai iya jefawa ƙuri’arsa ba tare da an ba shi ko sisin kwabo ba. Har ila yau, janar Buhari ne kawai wanda ko ka san kuskurensa, kake tsoron furta shi a gaban al’umma komai kyakkyawar manufar da kake da ita a cikin furta zancen. Wannan kuwa, domin Buhari ne kawai ɗan siyasar da ake iya cewa alhairinsa ya fi sharrinsa yawa kai tsaye. Continue reading →