Monthly Archives: August, 2013

Musulmi na gari da ke kan Sunnar Manzon Allah SAW (1)

Tare da Nasir Abbas Babi
Da sunan Allah mai rahama mai jinqai.
Musulunci addini ne na gari, kuma addini na gaskiya da ma’abuta shi ya kamata suyi alfahari da samunsa a matsayin addini. Wannan ce ta sanya duk wanda yake kiran kansa da sunan musulmi, ransa yakan vaci matuqa idan ka kira shi da wani suna da ke nuna cewar shi ba musulmi ba ne. Kamar ka kira shi da arne ko kafiri, mushuruki da sauransu.
Ba kowane musulmi ne cikakken musulmi ba, kuma ba kowane musulmi ne ke iya amsa sunan musulmi na gari ba. Amma dai duk musulmi, yana nan a matsayinsa musulmi kuma cikin lemar musulunci, madamar bai aikata wani aiki ko ya furta wata Magana wadda Allah da manzonsa suka tabbatar da aikin ko kuma maganar sun fitar da wanda ya aikata hakan daga musulunci ba. Musulunci addini ne na Allah. Don haka babu mai hurumin korar wani daga ciki, sai dai shi mutum ya kori kansa, ko kuma idan shari’ar Allah da manzon Allah ta kore shi.
Musulmi na gari shi ne, mai wankakkar zuciya mai cike da aminci. Ya kasance ba ya nufin kowa da sharri sai dai soyayya. Saboda addinin musulunci bai yarda ka cutar da koda mutum marar addini ba ballai kirista. Koda yaushe musulmi na gari za ka same shi mai son ci gaban al’umma ne ba mai neman tarwatsewarta ba. Koda yaushe zai kasance a cikin yin maraba da annashawa da sauran jama’ar da ya san su ko kuma bai sansu ba.
Musulmi na gari, shi ne wanda ya kasance mai horo da aikata alkhairi tare da hani zuwa ga aikata sharri. Kuma ya kasance mai karvar horo idan an hore shi da aikata alhairin, kuma mai hanuwa idan an hane shi zuwa aikata sharri. Ya kasance mai kamanta adalci da kuma tsare gaskiya a cikin hulxarsa da sauran al’umma. Musulmin kirki ne yake kasancewa tamkar wata mavuvvuga ta alkhairi ga mutane, yana mai gurin koda yaushe al’umma su qaru da alkhairukansa. Kuma ya kasance mai taushin zuciyar da take cike da tausayi ga al’umma.
Musulmi na gari, shi ne musulmin da bai kasance juji matattarar shara ba! Waton bai yarda ya wulaqanta kansa da sunan Tawadu’i (qasqantar da kai) ba. Wajibi ne ya kasance mai nuna girman kansa da qimarsa ga duk wanda yake ganin cewar shi babba ne ko kuma ya isa dole a yi biyayya a bayansa. A irin wannan hali kam, musulmi ba zai wulaqanta kansa ba, ba zai sassauta ba, ba kuma zai xaga qafa ba, ba kuma zai yadda ya bar kafar reni ba. Duk wani mai girman kai da ji-ji da kai, bai dace a samu musulmin kirki yana yi masabiyayya ba.
Musulmi na gari shi ne wanda zai kasance tamkar ruwa saboda sauqin lamarinsa, kuma ya zamo tamkar takobi gayawa jini na wuce saboda kaifinsa! Ya kasance tamkar tauraruwa mai haske ga al’umma, kuma idan an zo fagen bayarda shaidu ko faxar gaskiya, sai ya zamo tamkar makaho ta yadda ba zai gane nashi ko wanda ba nashi ba. Saboda haka ake son Musulmin kirki ya kasance Hasken da ke haskaka al’umma, a gefe xaya kuma ya zamo tamkar wuta mai zafi da quna.
Musulmi na gari shi ne wanda ya riqe littafen Allah sau da qafa, yana mai shedar cewa babu wata shari’a mafificiya akan shari’arsa (Allah) Kuma Annabi Muhammad mai tsira da aminci ya kasance abin koyinsa ga dukkan al’amurra! Ya riqe dukkan musulmai a matsayin ‘yan’uwansa da yake iya baiwa kariya a kowane lokaci. Ya kuma riqe tsoron Allah Ya kasance masa garkuwa kuma guzuri a kowane lokaci.
Musulmi na gari shi ne musulmin da zuciyarsa ta kasance cike da tsoron Allah. Ayyukansa da zantukansa suka kasance a cikin ambaton Allah dare da rana. Ya kasance mai fara kowane al’amari da ambaton sunan Allah, idan kuma ya cika ya kasance mai godiya ga Allah! Koda yaushe ya zamo mai kwaxayi da neman Allah Ya shiryar da shi zuwa ga hanya madaidaiciya, bisa ga kasancewar duk yadda kake ganin kamar kana rayuwa akan gaskiya, ba lallai ba ne ya kasance a gurin Allah ma haka kake.
Musulmi na gari shi ne wanda rayuwarsa ta kasance yana yin ta ne saboda Allah shi kaxai, ba wanda yake rayuwa saboda wasu guruka na duniya da ya saka a gabansa ba. Ya kasance mai fatar idan mutuwarsa ta zo, to koma ta wace hanya ce, mutuwar ta kasance akan tafarkin Allah ne kai tsaye. Musulmin kirki yakan kasance ba ya tsoron kowa sai Allah. Ba ya neman kowace alfarma ga wani Dan’adam face Allah!
Wannan hanyar ita ce hanyar gaskiya! Ita ce hanyar Allah marar kwana ko lungu! Ita ce hanyar da kowane mutum ya kamata ya kasance akanta. Wanda kuma duk ya xauki wata wadda ba ita ba, kuma har yake ganin idan ba an bi shi ba to ba za a dace ba, lalle ya zo da wani al’amari na daban. Kuma ya bi hanyar da ba za ta fitar da shi ba. Babu wanda aka ce dole abi shi sai manzon Allah SAW! To amma kuma ba za ka san manzon Allah ba sai ka je makaranta, don haka, musulmai na gari mu koma makaranta. Kafirta juna da zagin magabata ba aikin musulmin kirki ba ne.
Cikakken ahlussunna shi ne, wanda yake biye da dokokin Allah sau da qafa akan hanyar Manzon Rahama. Shi kuma dan bidi’a shi ne mai take hadisin manzon Allah ingantacce idan ya sava wa tunaninsa ko aqidarsa. Don haka a kowane lungu da saqo na musulmai akan samu ahlussunna kuma akan samu ‘yan bidi’a. Jama’ar musulmi mu koma makaranta. Ya Allah ka sanya mu cikin musulmi na gari da ke kan sunnar Manzon Allah SAW.
Za mu ci gaba