Monthly Archives: March, 2015

Kibiyar Tsautasyi (2)

kibiyar tsautsayiCi gaba daga inda muka tsaya a kashi na daya

Hankalin Ladidi ya yi matukar tashi sanadiyar wadannan tambayoyi, domin ta san ko shakka babu wani al’amari mai muni ya faru da kawarta. Amma sai ta yi kamar ba ta fahimci wani abu ne ya faru ba. Kai tsaye ta shawarci Lubabatu da su je wajen malam domin samun amsoshin tambayoyin. Nan take suka sulale daga gidan bukin ba tare da kowa ya sani ba. Continue reading →

Kibiyar Tsautsayi 1

kibiyar tsautsayi

Ba sai an gaya maka ba, yanayin zaman zugum din da ke ci gaba da wanzuwa tsakanin Alhaji Bala da matarsa Ladidi, tare da ’yarsu Zuwaira wadda ke gefe daya tamkar ruwa ya cinye ta ne, zai tabbatar maka da cewar ba lafiya ba!
“Zama hakan fa ba zai kawo wani sauyi daga wannan tsautsayi da ya same mu ba, ta yaya za a ce yarinyar nan na da juna biyu kuma har ya kai watanni biyu ba tare da mun sani ba?’’ Ladidi ce ta fadi hakan a lokacin da Alhaji Bala ya kura mata idanuwa cike da son ya dora alhakin wannan sakacin a kan ta.
Abin da Alhaji Bala bai sani ba shi ne, Continue reading →