Monthly Archives: February, 2013

Tirka-tirkar mulki a Najeriya: Idan kunne ya ji…

Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai.
Duk da dai Hausawa sun ce ba a shedar dan kuturu har sai ya girma da yatsunsa, amma wannan karo na shaide shi tun bai hada shekara ba. Shi ma saboda wata maganar Bahaushen mai cewa, kyakkyawar safiya tun daga marecenta ake ganewa kuma ko banza, maigirma Janar Muhammadu Buhari ya ba mu labarin cewa “Jiki magayi.” Saboda haka ina da tabbacin cewa, bari ba shegiya ba ce da ubanta; fiye da yadda na yi imani da cewa, masara idan ta ji wuta ita ke fadi. To, wane dare ne jemage bai gani ba? Continue reading →

MUHIMMANCIN YAREN LARABCI

IMG_20130203_165726Daga Makarantar Adiya Al-Islamiyya

(Lahadi 23/3/ 1434 A.H, 3/2/2013 CE)

Wannan ita ce makalar da daliban aji hudu na Adiya al-islamiya suka gabatar a ranar Assabar 23/3/ 1434 A.H, sun gabatar da ita ne a saman Assembly kamar yadda aka saba. Naja’atu Isma’il ce ta karanta takardar larabci, a yayin da Zubaida Almustapha ta gabatar da wannan fassarar, dukansu daga (class 4d). karkashin jagorancin malamin Ajin, Malan Maccido Isah. Kuma sun samu ta’alikat daga dalibai kamar su Fauziya Garb, Aishatu Rufa’I, Sha’awanatu Wadata. A sha karatu lafiya. Continue reading →

Daga Makarantar Adiya Al-Islamiyya

Daga Makarantar Adiya Al-Islamiyya

(Assabar 22/3/ 1434 A.H, 2/2/2013 CE)IMG_20130203_165726

Wannan ita ce maqalar da daliban aji hudu na adiya al-islamiya suka gabatar a ranar Assabar 22/3/ 1434 A.H, sun gabatar da ita ne a saman Assembly kamar yadda aka saba. Zainab Aminu (class 4d) ce ta jagoranci gabatarwar. karkashin jagorancin malamin Ajin, Malan Maccido Isah. ta kuma samu ta’aliqat daga dalibai kamar su Saratu Husaini, Karima Nuhu, Laisusa Aqilu da kuma Nusaiba Ahmad. A sha karatu lafiya. Continue reading →

TAHAZIBUL INSANI MIN KHISALISH SHAIDAN (2)

Tareda Nata’ala Sambo Babi (Nasaba)
08096967800-08063673656-08056878792

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira
da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad Shugaban Ma’aika, da iyalin gidansa, da kuma sahabbansa.

Bayan haka, wannan shi ne littafin TAHZIBUL – INSAN MIN KHISALISH – SHAIDAN.(wato tsarkake mutum daga halayen shaidan) Littafin Ya kunshi gabatarwa da fasalai guda uku da kuma Hatama. (cikasawa)

GABATARWA A GAME DA HALAYEN ZUCIYA Continue reading →

TAHAZIBUL INSANI MIN KHISALISSHAIDAN

Kashi na farko (1)
Tareda Nata’ala Sambo Babi (Nasaba)
08096967800-08063673656-08056878792
Nsbgroup2000@gmail.com
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai. Godiya ta tabatta ga Allah Mai tsarkake zuciya daga tsatsar aibobi, tsarki ya tabbatar masa mamallakin kowa da komai.
Tsira da amincin Allah su tabatta ga shugaban masu tsarkin zuciya. Shine Annabi muhammadu dan Abdullahi(S.A.W) Shugabban Manzani, cikamakin Annabawa, Shugaban Halitta, Tsira da Amincin Allah su tabatta agare shi, da iyalan gidansa Tsarkakakku, da Sahabbansa Zababbu.
Babu shakka cewa hakika ilimin Tsarkin Zuciya Ilimine wanda kowane Dan Adam yana da bukatuwa izuwa gareshi. bayan sanin alkur’ani da ilimin sanin Hadisi, to lallai sai neman ilimin (tazkiyah) wato ilimin tsarkake zuciya, wanda tsarkake zuciya ya na daga cikin abubuwan da Allah (S.W.T) ya aiko Annabinsa domin ya yiwa al’umarsa shi,
Allah (S.W.T) yace acikin littafen sa mai tsarki
Abinda yake a cikin Sammai da abinda ya ke acikin kassai suna yin tasbihi ga Allah mammallaki. Mai tsark, Mabuwayi, Mai Hikima. shine wanda ya aiko acikin Ummiyin (Marasa Rubutu da Karatu)wani Manzo daga garesu (Annabi Muhammadu)yana karanta ayoyin Allah akkansu. kuma ya na sanar da su littafe da hikima. da ya ke sun kasance gabaninsa suna cikin bata mabayyaniy) suratul jumu’ah 1-2

Kuma yace :- Na rantse da mutum da wanda ya daidaita halittarsa ya kimsa masa sabon sa da tsoron sa ga (Allah) lallai wanda ya yi kokarin tsarkake zuciyarsa ya dace, wanda ya cusa mata aikin sabo ya tabe,
suratul shams 7-10
Kuma Annabi (S.A.W.) yace
A cikin jiki akwai wata tsoka wacce idan ta gyaru to dukkan jiki ma sai ya gyaru, idan
kuwa tabaci to dukan jiki ma sai ya baci,wanan tsokar itace zuciya.
Bukhari da muslim ne suka ruwaito shi.
Kuma Annabi (S.A.W) ya ce
hakika zuciya tana yin tsatsa kamar yadda karfe ya ke yin tsatsa. abinda ya ke wanke ta, shine Ambaton Allah (zikiri).
To akan haka ne Annabi (S.A.W.) ya yiwa sahabban sa wannan gagarumin aiki. Su kuwa suka yi wa Tabi’ai, su kuwa suka yiwa tabi’u tabi’en, su kuma suka yiwa salihan Bayin Allah kamar salafus salih da waliyyai da sauran su. Wannan ne kuma ya sanya su ma mallamai suka dage kwarai da gaske wajen yiwa nasu jama’a wanna gagarumin aikin, kasancewar mallamai sune magada annabawa, kamar yadda yazo ahadisi Mallamai sunyi wannan gagarumin aikin ne ta hanyar da suka ga ya cancanci su yiwa na su jama’ar ya yin da wadansu daga cikin su, suka rubuta litafai da dama domin barwa wadanda zasu taso.
Daga cikin wadannan littafai akwai:-
• Ilmul kulubi, Abu Dalibul Makiy.
• Makashifatul kulubi, hujjatul islami Abu Hamidul Gazali.
• Qutul kulubi, Abu Dalibul Makiy.
• Arisala, Imamul kushairi.
• Ihya’u Ulumidden, hujjatul islam Abu hamidul Gazali.
To wanna dalilin ne shima wani bawan Allah, daga cikin manyan malamman wanna yankin namu na afrika, Mallami, kuma waliyi, masanin Alkur’ani da hadisi, fikhu da nahawu, kuma shakiki ga sheikh
Usmanu bin Fodiyo,(R.A.). mai suna Abdullahi bin fodiyo, wanda ake yiwa alkunya da Abdullahi Gwandu, ya rubuta wani wani litatfe mai albarka, wanda ya sanyawa suna TAHAZIBUL INSANI MIN KHISALISH SHAIDAN (tsarkake mutum daga halayen shaidan) Wannan littafe ya kunshi bayani ne akan yadda halin zuciya yak e da kuma fasulla gida uku.
1. Fassali na farko yana bayani ne akan hanyoyin da shaidan ya ke bi ya shiga cikin zuciya.
2. Fassali na biyu, yana bayani ne akan kashe-kashen zukata, yadda zukata suka rarrabu suka bambanta. Ma’ana mai tsoron Allah, da wacca ta lallace kwata-kwata, da wadda take tsaka tsaki.
3. Fassali na uku ya na bayani ne akan yadda za’a horar da zuciya ayi mata tarbiya, kuma a tsarkake ta daga cututtuka. Sai kuma hatama (cikawa) inda shekh Abdullahi gwandu, ya yi bayani agame da yadda za’a yiwa yara tarbiyya, har su girma cikin kyakyawan halaye da nagarta.
Babbu shaka duk da kasancewar wannan littafe karami, to amma yana kunshe da abubuwa masu muhimmanci agaremu, har dai awannan lokaci da al’umma ta lallace sabili da lallacewar zukata. Akarshe ina rokon Allah (S.W.T.) da ya yi gafara ga mawallafin wannan littafe, Abdullahi Gwandu, Allah ya dada haskaka masa kabarinsa, dashi da ya yansa Sheikh Usmanu bin Fodiyo Mujaddidu zaman, ni kuma Allah ka yafe mini kura-kuran da wata kila na yi wajen fassara wannan littafe, tare da kwadayin ladar Abin da na fassara dai-dai, Allah ka amfanar da mu abinda ya ke a cikin wanna littafe, Allah Ya yiwa iyayenmu gafara, ni da ku gabaki daya, Amin suma Amin. Allah dai ya taimake mu, ya bamu yawancin rai, da kwanciyar Hankali awannan kasar tamu ta nijeriya. Kuma Allah ya taimake mu Amin, domin alfarmar Ma’aiki (S.A.W) wassalam.

GABATARWAR ZAUREN FIKHU

Da sunan Allah mai rahama mai jinkai.

A wannan sashe za mu rika kawo muku amsoshi da tambayoyi akan abin da ya shafi Fikhu. Amma tambayouin da aka yiwa malamai suka amsa, ba wadanda aka tsinta akan hanya ba.

GABATARWAR HUDUBAR MALAMAI DAGA MUNBARI

Wannan sahe zai rika kawo muku Hudubar da malamai suke gabatarwa ne daga Masallatai daban-daban. Wannan kuma zai hada har da malamai magabata da hudubobinsu.

Za ka iya aiko muna abin da hudubar masallacinku ta kunsa domin mu wallafa muku. Allah ya sa mu dace.