Monthly Archives: July, 2013

Dare Mafi Tsada a Cikin Rayuwar Musulmi

Da sunan Allah mai rahama mai jin’kai.
Lailatul ‘kadari, ko kuma daren lailatul ‘kadari kamar yadda mu Hausawa muka fi kiransa, shi ne dare mafi tsada a cikin kowace shekara ta Allah kamar yadda malamai daban-daban suka bayyana a cikin tafsirin surar al’kur’ani ta (97 aya ta 3.) Haka ma hadisai da dama sun tuzgo suna Magana akan wannan dare mai alfarma. A cikin waccan ayar, Allah Mai girma da d’aukaka ya bayyana muna cewa, Lailatul ‘kadari tafi wata dubu alkhairi. Duk wani abu da za mu aikata na alkhairi, tun daga kan karatun Al’kur’ani mai girma, sallar nafiloli, ambaton Allah da sauransu a wannan dare, to ya fi alkhairi bisa ga yin wata dubu muna aikata su. To Allah Ya sa mu dace.
Da yawa malamai sun tafka muhawara akan ko yaushe ne Lailatul ‘kadari? Continue reading →

Ramadana sai watarana

Ramadana sai watarana
Da sunan Allah mai rahama mai jin’kai.
Tun kamar wata uku da suka wuce musulmin duniya gabad’aya hankalinmu ya karkata ga isowar wannan wata mai alfarma da nake shirin yi wa bankwana a halin yanzu. Mun kasance dukanmu muna masu addu’a da d’aukin cewa ‘’Ya Allah Ka nuna muna isowar wannan wata na Ramadana’’ To cikin ikon Allah ga mu tsundum a cikinsa, alamar da ke nuna cewa kafin gobe kuma, za ka ji an fara fad’in yau saura wata biyu a fara azumin gari duka (Ramadan). To sai dai kuma, shin muna tafiyar da wannan wata mai alfarma kamar yadda ya dace a tafiyar da shi? Ko kuma muna nan mun saki baki muna jiran sai wata shekara idan ya sake dawowa?
Ya ‘yan’uwa musulmi, muji tsoron Allah! Mu sani watan Ramadana rahama ne da jin’kai ga wannan al’umma, saboda haka ya zama wajibi akanmu, mu kiyaye ha’k’ko’kinsa. Daga cikin wad’annan ha’k’ko’kin kuwa harda kame harshenmu daga ambaton dukkan wani mutum da sharri, mu kame harshenmu daga miyagun kalamai, kalamai na Allah wadai marasa amfani. Ya ishi mutum hasara ya saki harshensa yana ta fad’ar duk abinda yake son fad’a ba tare da la’akari da amfani ko rashin amfanin abinda yake cewar ba. Irin wannan hali yakan sanya mutum cikin wad’anda suka yi hasara maimakon cin riba a wannan wata.
Ya ku bayin Allah, mu tuna da zancen manzo SAW a inda yake cewa: ‘’ Duk wanda watan Ramadana ya shigo bai yi wani abu da Allah zai gafarta mashi ba, Allah Ya nisanta shi ga rahama.’’ Ashe ko maimakon mu saki baki zuwa surutu, ya fi dacewa ne mu juyar da harshenmu zuwa ga ambaton Allah, neman gafara da horo da aikata khairi. Kwana ashirin da tara ne ko talatin kacal, idan mun kasa kame kanmu a wannan wata, ashe ba mu san yadda za mu tafiyar da sauran watanni goma sha d’aya na bayan Ramadana ba.
Ya ku ‘yan’uwana na jini da na musulunci, ku zo mu gudu tare mu tsira tare! Addu’ar manzon Allah kar’ba’b’biya ce. Kuma babu shakka, ba ‘karamar hasara ba ce, ace irin wannan wata ya shigo mutum bai samu kusanta ga Allah ba. To har yaushe muke shirin samun kusanta a gurin Allah idan mun kasa samu a wannan wata? Zuciyoyinmu suna yaudararmu ta hanyar nuna muna cewa akwai sauran lokaci. Da yawa daga cikinmu akwai masu tunanin cewa su jira sai kwanakin goman ‘karshen wata sannan su kame kansu ko su dage ga ibada, wannan wani salon yaudara ne da zukatanmu suke riya muna. Duk abinda ya hana mu maida hankali a yanzu, shi ne abinda zai hana mu maida hankali idan wannan kwanakin ‘karshen suka zo.
Ya zama wajibi mu zare damtse ta hanyar ziyartar wuraren da ake karatun Al’kur’ani (Tafsiri) domin muji sa’kon Allah mai girma da ya aiko muna. Mu ri’ka salloli na nafila, mu yawaita karatun Al’kur’ani da bayarda sadaka. Mu sadar da zumunta mu tausayawa mai rauni. Mu kiyaye fa, bara wasu da su aka yi Ramadan, amma a wannan shekara an dawo ba dasu ba! Muma babu shakka za a zo wani watan ba tare da mu ba, hasalima babu mai tabbacin wannan ba shi ne watan Ramadan na ‘karshe a rayuwarmu ba.
Muna ro’kon Allah Ya arzittamu da alkhairukan wannan wata, Allah Ka sa muna cikin wad’anda za su ku’buta daga shiga wuta, Allah Ka sa wannan wata ya zama jin’kai da rahama garemu, Allah Ka sa ya zama sanadiyar had’uwar kawunan musulmi baki d’aya. ‘Yan’uwa sai mun sake had’uwa da ku a cikin wani rubutun daban, kai kuma RAMADANA SAI WATARANA.
Nasir Abbas Babi
08095654301
08033186727

Adiya Islamiyya

Adiya Islamiyya

Bukin karshen zango