Monthly Archives: June, 2013

Jami’an Tsaro Ku Daina Ba Mu Tsoro

Da sunan Allah mai rahama mai jin’kai.

Da yawa wani mutum za a dade ana rena mashi hankali, ana amfani da shi
don biyan wata bu’katar da shi ba amfaninsa take yi ba, amma duk ba
tare da ya gano ba. Sai dai wani lokaci da an samu wani ya fahimtar da
shi sai ka ga cikin ikon Allah ya gane kuma ya gamsu. Irin haka kuma
takan faru har ga mutane ma’abuta hankali da tunani.

Shi yasa nake amfani da wannan damar domin yin kira ga jami’an tsaron
Najeriya musamman ‘yansanda, su sani fa su ba bayin kowa ba ne!
Ma’aikatan gwamnati ne da aka dauke su don su kare ‘yanuwansu mutane,
kuma tare da haka ake bautar da su ana sa su aikata ba daidai ba ga
al’umma. Kuma abin haushi shi ne, bayan dukan wannan wahala da keta
haddin Allah da na jama’a da ake saka su yi musamman akan abin da ya
shafi siyasa da lokutan za’be, ‘karshe duk masifar da ta taso a kansu
take ‘karewa.

Ya kamata ‘yansanda su fahimci cewa ana ci da ha’k’kinsu, ana maida su
kamar wawaye a wannana ‘kasa ta Najeriya, an dauke su da sunan su bayar
da tsaro, kuma an dawo ana sanya su ba mutane tsoro! Kuma idan aka yi
la’akari da menene ha’ki’kanin aikin dansanda, za a ga cewa aiki ne mai
cike da tsafta da tsarki, wanda nake da tabbacin duk wani aikin
gwamnati ba wanda ya kai shi muhimmanci.

Daga cikin aikin dansanda akwai tabbatar da zaman lafiya.
Wane irin aikin gwamnati ne zai tafi ba tare da zaman lafiya ba? Ba na
da bu’katar sai kowa ya ba ni amsa, ni na san babu ita. Amma nawa ake
biyn dansanda a matsayin albashinsa? Nawa ake ba sauran ma’aikatan
gwamnati? Ba ina maganar kwamishinoni, chairmomi, masu bada shawara na
musamman ko ‘yanmajalisa ba, don duk wanda ya lalace a cikin harkar
aikin gwamnati ai bai kai wadannan da na ambata baya ba. Kuma abin
haushi wasu ne daga cikinsu ke saka ‘yansamda suna ba mutane tsoro
maimaikon tsaro.

Yanzu idan muka dubi gidajen da ake bawa ‘yansanda domin su
zauna da iyalansu, babu gidan da zai kai naira dubu dari bakwai! Kuma
wai gidan da mutum zai zauna da iyalansa ne fa! Gida sai kamar dakin
samari, duk da irin wannan gwarzon aiki da dansanda yake yi (wanda
yake wa ‘kasa na tabbatar da tsaro da wanda yake yi wa ‘yansiyasa na ba
mutane tsoro) amma sai ka ga dansiyasa ya gina makeken gidan da
filinsa ma ya kai na miliyan ashirin zuwa sama, kuma sai a dauki
dansanda a kai bakin garkar dansiyasar wai shi ne zai yi gadi. Kaico!

Rayuwar dansanda ce tafi zama cikin hatsari ko rayuwar dansiyasar da
ake cilastawa ba ‘yansiyasa tsaro don ya baiwa talakawa tsoro? Wannan
makeken gida na ‘yansiyasa ai ko babu maigadi a bakin garkar ba wanda
ma ya san yadda za a yi ya shige shi har ya yi ‘barna. Amma gidan
dansanda fa? Ga shi nan a bakin hanya, sai dai kawai da yake Allah na
karewa, sai ka ga ba abin da yake faruwa, shi yasa nake ba ‘yansanda
shawara da su san ciyon kansu.

Ya kai dansanda, ina ba ka shawara, kada ka sake cin amanar kowa akan
wani dansiyasa, kada ka sake bari a hada da kai a yi muna magudi a
ranar za’be. In ma son samu ne, ka taimaka a kawar da wadannan
azallumai don kai ma ka samu ‘yancin kanka. Ba wanda ya halicce ka
idan ba Allah ba, kuma babu mai iya yi maka komai idan ba Allah ba.
Kuma shi ne wanda za ka hadu da shi a ranar da babu wani mai cetonka
sai shi.

Ina ji maku tsoron zuwan lokacin da za a daina jin tsoronku, kun ga
dai Ko yanzu jama’a sun dade da renaku, wanda hakan ya sa ba su ganin
girmanku, kuma na san a duk wannan al’amari babu laifinku in ba
‘ko’karin faranta ran wanda ba ya son ku ba. Ai ba sai na fadi ba. Tun
ranar da ake mulkin demukuradiya a Najeriya wane alfanu ne ‘yansanda
suka samu wanda ya taka kara ya karya? kuma ina rantsuwa da Allah inda
babu hadin kan ‘yansanda gwamnati azzaluma ba ta isa ta ci za’be ba.
Don haka ya kamata ku gyara, abin da kuke ciki na tashin hankali
yanzu, duk sanadiyar ‘yansiyasar da kuke daurewa gindi ne. saboda haka
ku yi muna adalci ku yi wa kanku.

Da zaran kun yi ‘ko’karin ganin cewa ranar za’be ba ku takurawa kowa ba,
kun hana masu taka doka su taka doka, mu kuma muka fito muka za’bi
wadanda ya dace a za’ba, to ina mai tabbatar muku za ku fi kowa jin
dadi a Najeriya. Saboda za a baku ha’k’kukkanku, kuma a yi tsaye a
kyautata jin dadinku ta yadda za ku daina ro’kon mutane naira ashirin a
kan hanyoyi. Shikenan sai ‘kimarku da martaba ta dawo a idon mutane.
Abu guda ne zai sa haka ta faru, shi ne ku daina ba mu tsoro.

Yabo da godiya sun tabbata ga Allah

08095653401

08033186727