Category Archives: Sauran al’amurra.

Jami’an Tsaro Ku Daina Ba Mu Tsoro

Da sunan Allah mai rahama mai jin’kai.

Da yawa wani mutum za a dade ana rena mashi hankali, ana amfani da shi
don biyan wata bu’katar da shi ba amfaninsa take yi ba, amma duk ba
tare da ya gano ba. Sai dai wani lokaci da an samu wani ya fahimtar da
shi sai ka ga cikin ikon Allah ya gane kuma ya gamsu. Irin haka kuma
takan faru har ga mutane ma’abuta hankali da tunani.

Shi yasa nake amfani da wannan damar domin yin kira ga jami’an tsaron
Najeriya musamman ‘yansanda, su sani fa su ba bayin kowa ba ne!
Ma’aikatan gwamnati ne da aka dauke su don su kare ‘yanuwansu mutane,
kuma tare da haka ake bautar da su ana sa su aikata ba daidai ba ga
al’umma. Kuma abin haushi shi ne, bayan dukan wannan wahala da keta
haddin Allah da na jama’a da ake saka su yi musamman akan abin da ya
shafi siyasa da lokutan za’be, ‘karshe duk masifar da ta taso a kansu
take ‘karewa.

Ya kamata ‘yansanda su fahimci cewa ana ci da ha’k’kinsu, ana maida su
kamar wawaye a wannana ‘kasa ta Najeriya, an dauke su da sunan su bayar
da tsaro, kuma an dawo ana sanya su ba mutane tsoro! Kuma idan aka yi
la’akari da menene ha’ki’kanin aikin dansanda, za a ga cewa aiki ne mai
cike da tsafta da tsarki, wanda nake da tabbacin duk wani aikin
gwamnati ba wanda ya kai shi muhimmanci.

Daga cikin aikin dansanda akwai tabbatar da zaman lafiya.
Wane irin aikin gwamnati ne zai tafi ba tare da zaman lafiya ba? Ba na
da bu’katar sai kowa ya ba ni amsa, ni na san babu ita. Amma nawa ake
biyn dansanda a matsayin albashinsa? Nawa ake ba sauran ma’aikatan
gwamnati? Ba ina maganar kwamishinoni, chairmomi, masu bada shawara na
musamman ko ‘yanmajalisa ba, don duk wanda ya lalace a cikin harkar
aikin gwamnati ai bai kai wadannan da na ambata baya ba. Kuma abin
haushi wasu ne daga cikinsu ke saka ‘yansamda suna ba mutane tsoro
maimaikon tsaro.

Yanzu idan muka dubi gidajen da ake bawa ‘yansanda domin su
zauna da iyalansu, babu gidan da zai kai naira dubu dari bakwai! Kuma
wai gidan da mutum zai zauna da iyalansa ne fa! Gida sai kamar dakin
samari, duk da irin wannan gwarzon aiki da dansanda yake yi (wanda
yake wa ‘kasa na tabbatar da tsaro da wanda yake yi wa ‘yansiyasa na ba
mutane tsoro) amma sai ka ga dansiyasa ya gina makeken gidan da
filinsa ma ya kai na miliyan ashirin zuwa sama, kuma sai a dauki
dansanda a kai bakin garkar dansiyasar wai shi ne zai yi gadi. Kaico!

Rayuwar dansanda ce tafi zama cikin hatsari ko rayuwar dansiyasar da
ake cilastawa ba ‘yansiyasa tsaro don ya baiwa talakawa tsoro? Wannan
makeken gida na ‘yansiyasa ai ko babu maigadi a bakin garkar ba wanda
ma ya san yadda za a yi ya shige shi har ya yi ‘barna. Amma gidan
dansanda fa? Ga shi nan a bakin hanya, sai dai kawai da yake Allah na
karewa, sai ka ga ba abin da yake faruwa, shi yasa nake ba ‘yansanda
shawara da su san ciyon kansu.

Ya kai dansanda, ina ba ka shawara, kada ka sake cin amanar kowa akan
wani dansiyasa, kada ka sake bari a hada da kai a yi muna magudi a
ranar za’be. In ma son samu ne, ka taimaka a kawar da wadannan
azallumai don kai ma ka samu ‘yancin kanka. Ba wanda ya halicce ka
idan ba Allah ba, kuma babu mai iya yi maka komai idan ba Allah ba.
Kuma shi ne wanda za ka hadu da shi a ranar da babu wani mai cetonka
sai shi.

Ina ji maku tsoron zuwan lokacin da za a daina jin tsoronku, kun ga
dai Ko yanzu jama’a sun dade da renaku, wanda hakan ya sa ba su ganin
girmanku, kuma na san a duk wannan al’amari babu laifinku in ba
‘ko’karin faranta ran wanda ba ya son ku ba. Ai ba sai na fadi ba. Tun
ranar da ake mulkin demukuradiya a Najeriya wane alfanu ne ‘yansanda
suka samu wanda ya taka kara ya karya? kuma ina rantsuwa da Allah inda
babu hadin kan ‘yansanda gwamnati azzaluma ba ta isa ta ci za’be ba.
Don haka ya kamata ku gyara, abin da kuke ciki na tashin hankali
yanzu, duk sanadiyar ‘yansiyasar da kuke daurewa gindi ne. saboda haka
ku yi muna adalci ku yi wa kanku.

Da zaran kun yi ‘ko’karin ganin cewa ranar za’be ba ku takurawa kowa ba,
kun hana masu taka doka su taka doka, mu kuma muka fito muka za’bi
wadanda ya dace a za’ba, to ina mai tabbatar muku za ku fi kowa jin
dadi a Najeriya. Saboda za a baku ha’k’kukkanku, kuma a yi tsaye a
kyautata jin dadinku ta yadda za ku daina ro’kon mutane naira ashirin a
kan hanyoyi. Shikenan sai ‘kimarku da martaba ta dawo a idon mutane.
Abu guda ne zai sa haka ta faru, shi ne ku daina ba mu tsoro.

Yabo da godiya sun tabbata ga Allah

08095653401

08033186727

Kishi da kishiya (3)

Da sunan Allah mai rahama mai jin’kai
Idan ba’a manta ba, a rubutun da ya gabata mun tsaya ne daidai wani baitin wa’ka da yake cewa “WADDA ZA TA ZAN SANADIN TSIRA, A GARE NI TO ITA ZAN AURA, KYAWO DA KUD’D’I NA LURA, WATARAN SUKAN JANYO HASARA, GA AURE IDAN BA A DACE BA.” To idan zan yi tambaya shin wacece wannan matar da zata zam sanadin tsira ga mijinta, amsar ita ce, mace ta gari wadda ba zata had’a ka da wasu samari a lokacin neman aurenta ba. Ba mai kud’i ko d’iyar masu kud’i ba, haka ba mai kyawo ko mai ta’kama da aji ba, mai ilimin addini da kyawawan halaye ake nufi. Allah ya sa mu dace.
Bari mu duba yadda kishi da kishiya yake kasancewa a gefen mata. Saboda ba a tuya a manta da albasa! Kishi na mata ne kuma su ya kamata a barwa abinsu. Sai dai a gyara musu kurakuran da suke cin karo da su da sunan kishi, har su je suyi ta ‘bata gishiri wurin dahuwar ‘kaho. Su ‘bata goma d’aya ba ta gyaru ba, kai harma su kan rasa Gira wurin gyaran Ido.
Wurin da kishi yake samun zama shi ne, wurin da aka ce mutum fiye da d’aya su yi tarayya a cikin neman abu d’aya. Kenan mace tana da dalilin yin kishi, sai dai ace ba ta yi shi daidai ba. Misali a fagen neman ilimi, sarauta, wani mu’kami ko neman kud’i, mutane da yawa ne suke neman wannan abin guda d’aya kacal, wanda duk ya kwantar da hankalinshi tsakani da Allah ba hassada ba kushewa ko sharri ga abokin da suke neman abinnan tare, ‘karshe cikin ikon Allah sai ka ga shine ya yi nasara.
Da kud’i da ilmi da mulki duka na Allah ne, ‘ko’kari da zafin nema ko rigima ba za su ta’ba sanya wani ya samu ko d’aya daga cikinsu ba sai Allah mad’aukakin sarki ya lamunce masa. Haka shima mijin da wata mace ta ke aure da shi ko za ta aura. Duk masifar da take tunani ko dubara da wasu shawarwari na miyagun ‘kawaye da za su iya ba ta domin ganin ta mallake mijin ita kad’ai, to babu wani tasiri da suke iya yi face idan Allah ya yarda. Ashe ko da mace ta wahalar da kanta tana ‘bata ma kanta lokaci, gara ta fara komawa Allah Ta’ala.
Tun farkon al’amari, Allah (S.W.T) ne ya amincewa mace ta zauna da namiji d’aya a matsayin mijinta, namiji kuma ya auri mace hud’u idan ya samu iko. Ko shakka babu, Allah ya fi mu sanin hikimar da ke cikin hakan. Saboda haka babu abin da ya rage ma kowa face mi’ka wuya ga al’amarin Allah kai tsaye. Idan kuma akwai wata mai dubarar da take ganin za ta iya fitar da kanta daga wannan tsari da Allah ya tsara, ‘kila ta hanyar shiga malamai (Bokaye) ko ‘kullawa abukkiyar zamanta sharri, yin hijira ta koma gidansu don mijinta zai auro wata macen ko d’aukar matakin muzgunawa miji don ya saki wadda ya aura ko ya fasa auren wadda zai aura, sai mu ce “GA FILI GA MAI DOKI.” Mun dai tabbatar da cewa har a nad’e duniya Allah da hukuncinsa ne masu rinjaye akan kowa! Kuma bayan duniya akwai lahira! Ranar da Allah zai tambayi kowa abin da ya aikata a duniya.
Yadda mata suke gudanar da zamantakewarsu a yanzu, ba zan so in kira hakan da sunan kishi ba. A zahirin gaskiya idan muka dubi abin za mu ga hassada ce tsantsa da ‘kiyayya! Kuma ma’aikin Allah yana cewa “HASSADA TANA CINYE KYAKKYWAN AYUKKA TAMKAR YADDA WUTA TA KE CIN KARMAMI” Ashe akwai had’ari mai girma a gurin macen da take irin wannan hassadar da sunan kishi komai kyakkywan ayukkan da take aikatawa.
Idan aka haifi yarinya tana ita kad’ai a gidansu har ta girma, duk ranar da mahaifiyarta ta ‘kara haihuwa, za ka samu farinciki take yi ta samu ‘kanwa. Da ita kad’aice misali, komai na alkhairi da kyautatawa ita ita kad’ai za a yi wa. Yanzu da aka samu ‘karin haihuwa sun zama su biyu, don haka su biyu za a ri’ka yi wa. Za su yi tarayya a cikin abu guda kenan. To ga shi tana farinciki da aka haifi wadda za ta zamo mata abukkiyar tarayya a cikin gida! To amma idan ta yi aure, a ka ce za a auro wata matar, ita ma tazo ta ci arzi’kin mijin kamar yadda ita ma take ci, sai labarin ya canza.
Macen da ba ta son wata ta zauna da mijinta, wane dalili ne take da shi idan ba hassada ba? Aure magana ce ta shari’a ba son rai ba. Shari’ar nan ita ce ta amince da a auro wadda a ka auro ta farin, kuma ita ce ta yarda a yi mata duk abin da minjin yake yi mata, tun daga kan ciyarwa, shayarwa, tufatarwa harma da kwanciyar aure da miji yake yi da matarsa. Har ila yau shari’ar nan ce ta amince da a auro wata matar a had’a tare da waccan ta farko su zama su biyu. Mace ta yarda da tayi zaman aure bisa ga tsari na shari’a, amma ba ta yarda a uro wata su zauna bisa ga tsari na shari’a ba? Ai wanna hassada ce har ma da hauka?
Tabbas akwai lokutan da mazan ne suke ‘karo aure a lokacin da bai dace ba, ko kuma suke rashin adalci a tsakanin mata biyu ko fiye, kuma wanna matsala ce ta daban wadda za mu yi maganarta daga baya.
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah
Nasir Abbas Babi
08095653401
08033186727

Kamanta ‘Yan Fim Da Malaman Addini Da’ki’kanci ne

Da sunan Allah mai rahama mai jin’kai.
A kowace rana ko safiya ta Allah wani sabon al’amari kake jin yana fitowa daga wad’anda ba ka yi tsammani ko zato ba! A rayuwa akwai ban tausayi, idan ka ga mutum da siffar masu ‘kima amma kalamansa su ri’ka kasancewa na mahaukata tuburan. Babu wata hauka da take da ban tausayi a cikin nau’ukan hauka wadda ta kai haukar da mai ita bai yadda shi mahaukaci ba ne. Continue reading →

Barka da zuwan ma’aikacinmu.

3f2c4e0e07b81ff3
Muna bukatar dukan Admins dinmu da ke aiki da mu a shafin Tumbin Giwa na Facebook da su cike wannan Form din.

Ba mu da bukatar mata ‘yan Jarida

Ba mu da bukatar mata ‘yan Jarida: Martani ga Madina Dauda
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai.
A wata hira da leadership Hausa ta yi da kwararriyar ma’aikaciyar
gidan rediyon muryar America (VOA), mai suna Madina Dauda, ta bayyana
cewa tana takaicin karamcin mata a aikin Jarida. Kuma a zahirin
gaskiya ni dai wannan furuci nata bai yi min dadi ba. Saboda Continue reading →

Tirka-tirkar mulki a Najeriya: Idan kunne ya ji…

Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai.
Duk da dai Hausawa sun ce ba a shedar dan kuturu har sai ya girma da yatsunsa, amma wannan karo na shaide shi tun bai hada shekara ba. Shi ma saboda wata maganar Bahaushen mai cewa, kyakkyawar safiya tun daga marecenta ake ganewa kuma ko banza, maigirma Janar Muhammadu Buhari ya ba mu labarin cewa “Jiki magayi.” Saboda haka ina da tabbacin cewa, bari ba shegiya ba ce da ubanta; fiye da yadda na yi imani da cewa, masara idan ta ji wuta ita ke fadi. To, wane dare ne jemage bai gani ba? Continue reading →

WASIƘA ZUWAGA SABON SARDAUNA

2

Yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai juya zamani, tsira da aminci su tabbata ga Annabin Allah Muhammad (S.A.W) wanda yafi kowa imani.   Assalamu Alaikum.
Ranka ya ɗaɗe, a gurguje ya kamata in rubuta maka wannan takarda, kuma a cikin taƙaice abubuwa saboda ƙaramcin lokaci.
kamar dai yanda ka sani cewa Sir Ahmadu Bello Sardauna ba shine kaɗai sardaunan da aka taɓayi a Najeriya ba, ko lokacinda yana raye ba shi kaɗai bane sardauna, yanzuma da baya duniya akwai wasu sardaunan da yawa. Amma dai idan har muna magana ne akan abinda ya shafi ci gaban ƙasa da gwa-gwar maya don ciyarda Arewa gaba, to da an faɗi Sardauna ka san wanda ake nufi domin guda ɗaya ne.
Tarihi bai sanar damu wani sardauna da akayi kafinshi ba, idanuwan mu basu ganar muna wani Sardauna a halin yanzu ba. Domin shi wancan Sardaunan har ya koma inda Allah ba’a zarge shi da kwashe dukiyar jama’ar da yake jagoranta ba, bai gina manya-manyan gidaje yattara tsadaddun motoci ba, baiyi amfani da muƙaminshi ta hanyar da bata dace ba, kamar zuwa ƙasa-shen waje yawon buɗe ido, ɗaukar diyanshi zuwa ƙasashen ketare domin yin karatu, ko kuma yasa a ɗaure wanda yaga dama ko aci zarafin wanda baya so.
Kasancewar ko yau ko gobe, ba zamu taba ɗebe rai akan samun wani jigo da zaiyi tsaye don ganin haƙar da gamji sardauna yayi ta cimma ruwa ba. Shi yasa na zari Alƙalami domin rubuto maka wannan takarda tare da fatar Allah yasa kaine Sardauna na biyu.
Na san duk wanda yace zaiyi koyi da wani magabaci, to haƙiƙa a dole ya kasance yayi kwaikwayon koda kaɗan daga cikin halayen wanda zai koya na alkhairi ko akasin hakan. Don haka mai halin mazan jiya sabon sardauna zanyi amfani da wannan damar ne don inyi maka tunatarwa akan wasu halayen Sir Ahmadu Bello Sardauna. Da kuma kura-kuran da shi kanshi ya samu, kasancewar shi ɗan Adam ne kamar kowa kuma zai iya yin kuskure.
Ina baka shawarar ka kasance sardauna mai neman kawo canji ga Najeriya baki ɗaya ba arewa kawai ba. Domin wanda ya ga bace ka yayi ƙoƙarin shine domin ci gaban Arewa. kuma ya samu nasarar hakan duk da cewa yanzu duk wata gina da yayi an rosa ta.
Kafin ka samu nasarar yin wannan aiki kuwa, na kawo canji a Najeriya baki ɗaya, akwai buƙatar kasa juriya da tsoron Allah a cikin rayuwar ka. Saboda irin wannan jan aiki ba zaiyiyu ba saida juriya da kuma tsarkake zuciya daga biyar son rai. Kuma ba’a samun haka saita hanyar dogaro ga Allah.
Kamar yanda kaima ka sani, kamar yanda kuma kowa ya sani cewa akwai mazaje a gabanka waɗanda tsayayyu ne, daga yankin Arewaci har yankin kudanci akwaisu, waɗanda duk wanda yake da manufar haɗa kan wannan ƙasa tazamo ƙasa guda a samu zaman lafiya, to zasu iya kawarda shi ta kowace hanya.
Kadaiji yanda aka kashe Kudirat Abiola ko?, kuma kaji yanda akayi aka bada cin hanci domin taushe wannan maganar ko? Kuma kaji waɗanda suka bayar da kuma waɗanda aka bawa ko?. To yayi kyau, wai don kasan wannan ƙasa akwai matsaloli waɗanda zasu iya maidaka mahaukaci inba ka kai zuciya nesa ba. Ka kuma san ko ina akwai miyagu.
Najeriya dai wata ƙasa ce guda ɗaya tak, wadda aka haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin sassa biyu na ƙasar domin a tabbatar da ta kafu. Amma gashi bayan kafuwar ta, sai wasu ƙadangarru suka ɗanyi amfani da wata kafa data tsage suka samu wurin shiga. Yanzu kuma yana daga cikin ayukkan dake gabanka sake yin tsaye domin haɗewar ta.
Nasan cewa muna cikin matsalar wutar lantarki da matsalar tsaro, matsalar Karamcin Ilimi da fannin lafiya, da dai matsaloli barka tai. Amma dai babban abinda yafi muhimmanci a yanzu shine a samu kyakkyawar fahimta tsakanin bangarorin biyu.
Yanzu ka duba ka ga wani lalaci da wata jam’iyyar siyasa ta ɓullo dashi, wai tsarin Karɓa-Karɓa. Wannan tsarin yaudara ce kawai a ciki da kuma neman ƙara raba kan Al’ummar ƙasa. Zanyi maka bayani dalla-dalla akan sherinda yake cikin wannan tsari a cikin takarda ta biyu.
Inda zaka ƙara gano aibin abar wannan ƙasa taci gaba da tafiya a bisa ɓangaranci, wannan ɓangaranci a tsakanin talakawa kawai yake. Kuma a tsakaninsu ne yake tafka mummunar ɓarna. Ka dubi abinda yake faruwa kwanannan akan ƁARAYIN TALLAFIN MAN FETUR, ai manyan mutane ne daga kudanci da kuma arewaci aka kama da wannan satar. Wannan satar tare suke yinta a lokaci ɗaya, tare suke zama a bawa kowa nashi kaso ba tareda anyi la’akari da ɓangaranci ba.
To kadubi Jos ka gani, talakawa ne keta kashe junansu a lokacinda waɗancan kurayen suke haɗe kai suna rabe dukiyar haramun a tsakanin su. Wannan bai ishemu wa’azi ba?.
Ko ka taɓa jin  ance sunje rabon kuɗi sunyi faɗa saboda anƙi rabawa dai-dai da wani saboda yana musulmi ko kirista?, ko kuma yana ɗan kudu ko Arewa?.
Allah yaja zamanin Sardauna, mu haɗu a takarda ta biyu domin maganar karɓa-karɓa da kuma ƙarin bayani.