Tirka-tirkar mulki a Najeriya: Idan kunne ya ji…

Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai.
Duk da dai Hausawa sun ce ba a shedar dan kuturu har sai ya girma da yatsunsa, amma wannan karo na shaide shi tun bai hada shekara ba. Shi ma saboda wata maganar Bahaushen mai cewa, kyakkyawar safiya tun daga marecenta ake ganewa kuma ko banza, maigirma Janar Muhammadu Buhari ya ba mu labarin cewa “Jiki magayi.” Saboda haka ina da tabbacin cewa, bari ba shegiya ba ce da ubanta; fiye da yadda na yi imani da cewa, masara idan ta ji wuta ita ke fadi. To, wane dare ne jemage bai gani ba?
Yadda alama take nunawa, mutanen Najeriya sun farga kuma sun lura da mugun kuskuren da suka tafka a zaben Shugaban kasa da ya gabata a 2011, kuma sun shirya tsaf domin ganin sun hanbare shegiyar uwa daga kan mulkin wannan kasa. Amma dai da sauran rina a kaba, don har yanzu muna yi wa darussan da muka koya daga zaben da ya gabata rikon sakainar kasha kuma wannan kuskure ne da kan iya sa mu sake ba da kai bori ya hau.
Duk dai ba a nan Gizo ke saka ba, wane mataki muke dauka domin ganin cewa shekara ta 2011 ba ta sake maimaita kanta ba? Ba na da bukatar mu bata lokaci wajen tattauna abin da ya faru a wancan lokacin. Mu tsaya mu yi nazari a kan abin da ya kamata mu aikata idan Allah Ya nufe mu da kasancewa cikin wadanda za su ga zaben 2015. Domin an ce kayan shiga ruwa, tun a tudu ake shirya su kuma mai zurfin ido da wuri yake fara kuka.
Kun san me ya sa nake muku zancen nan? Saboda a Najeriya, tsuntsun da ya ja ruwa ba shi kadai ruwan kan doka ba, har da tsuntsayen da ba su ji ba ba su gani ba. Kun ga dai ni ban zabi PDP ba, amma sai ga ni cikin layin masu zanga-zangar kin jinin janye tallafin man fetur, sai ga shi wata rana na kwana gefen titi randabawul din Abakwa, a hannun sojoji. Lokacin na je Kaduna ne, wai laifina shi ne, karfe shidda na yamma ya yi ban shige ba! A nan aka tara mu, har da wani Ustazu da wasu mata guda hudu. Cikinmu kuwa har da wasu ma’aikatan gidan ruwa guda biyu, da wasu dalibai da suka fito daga Makarantar Koyon Aikin Soja ta NDA.
A zaben shekara ta 2011, gwamnoninmu na Arewa da ke karkashin PDP ne suka yi ruwa suka yi tsaki, suka samar wa Jonathan kashi ashirin da biyar na kuri’un da aka jefa a jahohinsu. Wanda hakan ne ya ba shi damar tsallakewa ba tare ma da an je zabe karo na biyu ba. To, hukuncin da za mu yi musu shi ne: Ba za mu zabe su a 2015 ba, ba za mu zabi wadanda suka tsayar ba kuma ba za mu bari kowa ya zabe su ba ko da ta kama da karfin tsiya.
Ganin cewa da kyar da magudi aka hada wa Ebele kashi ashirin da biyar a kowace jiha, alama ce da ke nuna kashi saba’in da biyar sun san abin da suke yi. To, ya za a yi kashi ashirin da biyar su fi karfin kashi saba’in da biyar? Don haka taron dangi za a yi! Zancen wai kowa da ra’ayinsa ya zabi wanda yake so babu shi, ba haka ake yi a Najeriya ba mun dauki darasi. Magana ce ta kowa ya kama warinsa.
A matsayina na dan Shekara goma sha takwas, zan dauki alwashin duk tsarana da ke unguwarmu ba zan bar shi ya zabi PDP ba ko ta wane hali ne, haka ni ma dan shekara ashirin, ashirin da biyar, talatin, arba’in… saboda me? Saboda PDP ba alheri ba ce a gare mu. Kuma idan ya zabe ta, aka samu wani marar hankali da tunani irinsa a wata unguwa ya zabe ta, a haka sai a sake hada wasu kashi ashirin da biyar a ce Jonathan ya ci su. Har yanzu ke nan, inda aka tuma an sake faduwa nan.
Matayenmu da ake bin su da sabulun wanka da na wanki don su yi zabe, su ma dole ne mu hana su a zabe mai zuwa, ba wai kada su karba ba. Mu dai sanar da su duk wanda ya ba ku ku karba, amma kada ku sake zabensu. “Daman kudinku ne da suke sacewa suka fitar a yanzu, don haka kada ku bar mugu da makami, ku amshi duk abin da suka ba ku, amma ku zabi wanda zai taimake ku”
kauyukan da ake shiga ana yi musu wala-wala don ba su san komai ba, ya zama dole mu sadaukar da lokutanmu domin zuwa wadannan wurare muna wayar musu da kansu a kan hadarin da suke ciki. Mu zaburar da su, mu sanar da su abin da ba su sani ba, sannan mu ba su damar su kasa su tsare kada su bari ko hakimi ya taba. Idan hakimi ya jefa kuri’a ya je ya ba su wuri, babu mai kima sai wanda ya kama kimarsa a 2015. Idan hakimi ya karbo kudi ya kawo musu, su karba amma kada su yi mai biyayya, hakimi ai ba Allah ba ne!
Tabbas ba mu ne ke zaben PDP ba, amma dai abokanmu, kannenmu, yayyenmu da matayemu na birni da kauye su ne! Saboda haka ya zama dole mu hane su. Zancen lissafa kuri’a da bayyana sakamako ba na mu ba ne, aikinmu guda biyu ne kacal: Mu jefa kuri’a ga wanda ya dace, mu hana kowa jefa wa wanda bai dace a jefa mawa ba. Su kuma wadanda ya kamata su tsaya a lissafa a gabansu sai su dauka daga inda muka tsaya. In kunne ya ji, to gangar jiki ta tsira!
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah!

5 responses

  1. Ina mai yi maka sallama Assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuh dafatan kana cikin koshin lafiya a duk inda kake ko ,ni sunana muhammad sadiq daga garin yola fadar jahar adamawa kuma ni ma’aikacin gidan Radio ne da Tv a nan yola amma mai zaman kanta ne in bazaka damuba ina bukatar magana da kai sai dai ban ya abun zai kasance ba ni in ka gamsu ga number ta kamar haka 090 34 55 43 08 NAGODE .

  2. BISHIR MUSA DANJA | Reply

    ALLAH kai kasan karatun kurma najeria muna cikin halin rashin shuga banni masu adalci, kowa yasamu dagashi sai ya’yan shi, allah kaimana canji na alkairi, amin summa amin.

  3. Sai mun ta shi tsaye!

    1. Haka ne Malan Surajo. Allaah dai ya shige muna gaba..

Ka bar sakonka a nan