Monthly Archives: May, 2013

Kishi da kishiya (3)

Da sunan Allah mai rahama mai jin’kai
Idan ba’a manta ba, a rubutun da ya gabata mun tsaya ne daidai wani baitin wa’ka da yake cewa “WADDA ZA TA ZAN SANADIN TSIRA, A GARE NI TO ITA ZAN AURA, KYAWO DA KUD’D’I NA LURA, WATARAN SUKAN JANYO HASARA, GA AURE IDAN BA A DACE BA.” To idan zan yi tambaya shin wacece wannan matar da zata zam sanadin tsira ga mijinta, amsar ita ce, mace ta gari wadda ba zata had’a ka da wasu samari a lokacin neman aurenta ba. Ba mai kud’i ko d’iyar masu kud’i ba, haka ba mai kyawo ko mai ta’kama da aji ba, mai ilimin addini da kyawawan halaye ake nufi. Allah ya sa mu dace.
Bari mu duba yadda kishi da kishiya yake kasancewa a gefen mata. Saboda ba a tuya a manta da albasa! Kishi na mata ne kuma su ya kamata a barwa abinsu. Sai dai a gyara musu kurakuran da suke cin karo da su da sunan kishi, har su je suyi ta ‘bata gishiri wurin dahuwar ‘kaho. Su ‘bata goma d’aya ba ta gyaru ba, kai harma su kan rasa Gira wurin gyaran Ido.
Wurin da kishi yake samun zama shi ne, wurin da aka ce mutum fiye da d’aya su yi tarayya a cikin neman abu d’aya. Kenan mace tana da dalilin yin kishi, sai dai ace ba ta yi shi daidai ba. Misali a fagen neman ilimi, sarauta, wani mu’kami ko neman kud’i, mutane da yawa ne suke neman wannan abin guda d’aya kacal, wanda duk ya kwantar da hankalinshi tsakani da Allah ba hassada ba kushewa ko sharri ga abokin da suke neman abinnan tare, ‘karshe cikin ikon Allah sai ka ga shine ya yi nasara.
Da kud’i da ilmi da mulki duka na Allah ne, ‘ko’kari da zafin nema ko rigima ba za su ta’ba sanya wani ya samu ko d’aya daga cikinsu ba sai Allah mad’aukakin sarki ya lamunce masa. Haka shima mijin da wata mace ta ke aure da shi ko za ta aura. Duk masifar da take tunani ko dubara da wasu shawarwari na miyagun ‘kawaye da za su iya ba ta domin ganin ta mallake mijin ita kad’ai, to babu wani tasiri da suke iya yi face idan Allah ya yarda. Ashe ko da mace ta wahalar da kanta tana ‘bata ma kanta lokaci, gara ta fara komawa Allah Ta’ala.
Tun farkon al’amari, Allah (S.W.T) ne ya amincewa mace ta zauna da namiji d’aya a matsayin mijinta, namiji kuma ya auri mace hud’u idan ya samu iko. Ko shakka babu, Allah ya fi mu sanin hikimar da ke cikin hakan. Saboda haka babu abin da ya rage ma kowa face mi’ka wuya ga al’amarin Allah kai tsaye. Idan kuma akwai wata mai dubarar da take ganin za ta iya fitar da kanta daga wannan tsari da Allah ya tsara, ‘kila ta hanyar shiga malamai (Bokaye) ko ‘kullawa abukkiyar zamanta sharri, yin hijira ta koma gidansu don mijinta zai auro wata macen ko d’aukar matakin muzgunawa miji don ya saki wadda ya aura ko ya fasa auren wadda zai aura, sai mu ce “GA FILI GA MAI DOKI.” Mun dai tabbatar da cewa har a nad’e duniya Allah da hukuncinsa ne masu rinjaye akan kowa! Kuma bayan duniya akwai lahira! Ranar da Allah zai tambayi kowa abin da ya aikata a duniya.
Yadda mata suke gudanar da zamantakewarsu a yanzu, ba zan so in kira hakan da sunan kishi ba. A zahirin gaskiya idan muka dubi abin za mu ga hassada ce tsantsa da ‘kiyayya! Kuma ma’aikin Allah yana cewa “HASSADA TANA CINYE KYAKKYWAN AYUKKA TAMKAR YADDA WUTA TA KE CIN KARMAMI” Ashe akwai had’ari mai girma a gurin macen da take irin wannan hassadar da sunan kishi komai kyakkywan ayukkan da take aikatawa.
Idan aka haifi yarinya tana ita kad’ai a gidansu har ta girma, duk ranar da mahaifiyarta ta ‘kara haihuwa, za ka samu farinciki take yi ta samu ‘kanwa. Da ita kad’aice misali, komai na alkhairi da kyautatawa ita ita kad’ai za a yi wa. Yanzu da aka samu ‘karin haihuwa sun zama su biyu, don haka su biyu za a ri’ka yi wa. Za su yi tarayya a cikin abu guda kenan. To ga shi tana farinciki da aka haifi wadda za ta zamo mata abukkiyar tarayya a cikin gida! To amma idan ta yi aure, a ka ce za a auro wata matar, ita ma tazo ta ci arzi’kin mijin kamar yadda ita ma take ci, sai labarin ya canza.
Macen da ba ta son wata ta zauna da mijinta, wane dalili ne take da shi idan ba hassada ba? Aure magana ce ta shari’a ba son rai ba. Shari’ar nan ita ce ta amince da a auro wadda a ka auro ta farin, kuma ita ce ta yarda a yi mata duk abin da minjin yake yi mata, tun daga kan ciyarwa, shayarwa, tufatarwa harma da kwanciyar aure da miji yake yi da matarsa. Har ila yau shari’ar nan ce ta amince da a auro wata matar a had’a tare da waccan ta farko su zama su biyu. Mace ta yarda da tayi zaman aure bisa ga tsari na shari’a, amma ba ta yarda a uro wata su zauna bisa ga tsari na shari’a ba? Ai wanna hassada ce har ma da hauka?
Tabbas akwai lokutan da mazan ne suke ‘karo aure a lokacin da bai dace ba, ko kuma suke rashin adalci a tsakanin mata biyu ko fiye, kuma wanna matsala ce ta daban wadda za mu yi maganarta daga baya.
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah
Nasir Abbas Babi
08095653401
08033186727

Soyayya kafin aure: Kura ce da kan Rago (2)

Da sunan Allah mai rahama mai jin’kai.

A cikin rubutun da ya gabata mai taken: – SOYAYYA KAFIN AURE: KURA CE DA KAN RAGO (1) Na fara da bayanin rashin amfanin irin wannan soyayya (ta kafin aure) da matsalolinta, tare da soke wata gurguwar fahimta da muka dade muna yi a kanta (wai ana yin ta ne domin a fahimci halin juna), inda a ‘karshe na tsaya a wani baitin wa’ka mai cewa: –
“Ita gaskiya fa akwai daci, Zafinta ba shi da sassauci, Sai dai idan ga adalci, Ita ce Madubin dubawa”

Tambayar da wasu ke yi ita ce, wai ya za’a yi kaga yarinyar da ta kwanta maka a rai, kuma ace ka ‘kyale ta don ba ka tashi aure ba? To ni kuma sai nake tambayar su, me ya sa za ka ga mota mai kyau, wadda ta kwanta maka a rai, kuma kana matu’kar sha’awar ta, amma ka bari ta wuce ka? ‘Kila don ba ka da kudin sayen ta, ko kuma ba ka tashi sayen motar ba, to ai ita ma haka, dole ne ka barta idan har ba ka tashi aure ba, ko kuma Allah bai hore maka abin auren ta ba. Abin da ya kamata shine, ka ro’ki Allah ya ba ka wadda ta fi ta, kuma ya hore maka abinda za ka yi auren.

Idan dai har bariki kake so ka yi, to akwai y’an mata da yawa irin ka, sai kaje can kuyi barikinku, kafin ranar da Allah zai kar’bi rayukanku, ya kuma yi muku hisabi akan laifukanku. Amma dai, mu daina la’bewa ga aure muna yin yaudara.

Har ila yau, ya kamata mu gane cewa, tsananin son zuciya da ke cike da zukatanmu, tasirinsa ke sa muke neman mace ba tare da mun tashi aure ba. Haka kuma shine mai sawa, muke ganin tamkar wayewa ce mace da namiji su dai-daita kansu a tsakaninsu su kadai. A tawa fahimta, mahaifa ne ya kamata su yi ruwa su yi tsaki a cikin auren ‘ya’yansu.

Ban yarda da auren dole ba, haka ma ban yarda da auren sha’awa ba, saboda haka, ba ina nufin a yi wa yara auren dole ba, amma dai a za’bar ma yaro, yarinyar da aka yarda da kyawawan halayenta da addininta, wadda aka fahimci rayuwar su ta na kan ma’aunin da za su iya zama lafiya. Daman aikin yaro da yarinya bai wuce gano fuska mai kyawo ba.

Daga jin kalaman saurayi ga budurwarsa, ka san akwai ‘kuruciya da rashin sanin makoma a ciki. Wai sai kaji yana ce mata: – “Ni abin da yake burge ni da ke shine, kyawon surar da Allah ya yi miki, musamman fararen idanuwanki! Masoyiyata, tun ranar da na fara haduwa da ke, takawarki take matu’kar burge ni! Zubin jikinki ya yi min dai-dai, ga iya kwalliya, ga za’kin murya…..” ita kuma, daga jin haka, sai ka ga farinciki da nishadi ya lullu’be ta, wai an yabe ta. Jama’a ba haka ake firar ba? To duk abubuwan da ya jero mata dinnan, su ne manyan ababen bu’kata a cikin aure?

Kina da halayen kirki, kowa sai yabon dabi’arki yake yi, ga karatu da kaifin basira Allah ya ba ki. Babban abinda yake burge ni da ke, shine tsananin ri’kon addininki! So nawa ka ta’ba jin irin wadannan kalamai daga saurayi zuwa budurwarsa? To ashe dai idan aka ce yaro ya nemawa kansa aure, abu na farko da yake nema, yarinya kyakkyawa. ita kuma budurwa, abinda take dubi, ta samu mai kudi, ko wanda ya iya kalaman soyayya.

Bisa ga wadannan dalilai, sai muka ce a tuna da baya, shin mahaifa da kakanninmu da suke zaune lafiya a gidajen aure, shin sun yi irin wannan soyayyar ne? Ba haka suka yi ba. To ya ya su ka yi? Mahaifansu ne suka za’bar musu matan aure, kuma a haka suka zauna lafiya har suka haife mu.

Abu mai matu’kar tada hankali ne, yadda za ka ga yarinya ta isa aure, amma a ki aurar da ita. Wai sai ta ‘kare boko! Ko miye dalilin masu wannan al’ada? Oho, Allah masani.

Mahaifi da mahaifiya ku sani, ina yi muku wannan magana ne a cike da ladabi da girmamawa, amma dai, diyanku mata da suka balaga, su na da bu’katuwa izuwa ga namiji, ‘kila fiye da yadda ku kuke bu’katuwa ga junanku, haka su ma mazan. Sannan makarantar da kuke cilasta su sai sun yi, idan sun je ba ku san me suke yi ba! In dai ana zuwa ruwa, to wataran cilas ne sai an yi ‘bari. Manzo mai tsira da aminci ya bayyana muna, suturar mace guda biyu ce kawai: – ko dai tana cikin kabarinta, ko kuma gidan mijinta! To dubararka da shawararka ne mafita, ko zancen Manzo mai tsira da aminci? Kuji tsoron Allah mahaifanmu.

Yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki.