KYAWAWAN AYYUKA DA KYAWAWAN NIYYOYI

Bayan Malam ya girmama Allah da kirari mai girman gaske, ya kuma yi salati ga fiyayyen halitta da addu’a ga alayensa da sahabbansa da duk wanda suka biyo bayansu da kyautatawa.

‘Yan uwa Musulmi muji tsoron Allah, sannan mu duba ayyukan da muke gabatarwa kawunan mu na ayyuka da niyyoyi da muka kullata a zukatan mu domin Allah Jalla wa’ala ya halitta mu domin yaga wanene yafi kyakkyawan aiki a wannan rayuwa. Ta haka ne kuma Allah bai kyalemu ba sai da ya bayyana mana tafarkin Alhairi da kuma tafarkin sharri, sannan bayan ya bayyana wannan Allah yayi mana muwafaqa da kyawawan ayyuka dukkan wanda ya kullaci wata niyya a cikin zuciyarsa.

Mu sani cewar Allah madaukakin sarki ya shar’anta mana da ayyuka da niyya zasu zama sababin tsiran mutum komai lalacewarsa domin Allah Jalla wa’ala baya kallon surar mutane, baya kallon dukiyoyinsu saidai Allah yana kallon ayyukansu ne da kuma zukatansu. Kuma sakamako Allah yanayi ne daga abin da mutum ya kasance yana aikatawa. Abubuwan da muke gani anan, kamar yanda mutum yayi mu’amala haka Allah zaiyi mu’amala da shi, idan yayi mu’amala da Allah a bias alkhairi to Allah zai yimu’amala da shi a bias alkhairi tun a nan duniya sa’annan kuma idan yakoma ranar Qiyama yacika masa alkhairi. Idan kuma yayi mu’amala da shi ta sharri, to Allah zai mu’amalanceshi da misalin abin da yayi.

Annabi (S. A. W) yace Allah ya rubuta kwawawan ayyuka ya kuma rubuta munanan ayyuka, sannan ya bayyana wannan, duk wanda yayi niyyar aikata kyakkyawa amma bai aikata wannan kyakkyawan aikiba to Allah zai rubuta masa wannan a matsayin kyakkyawan aiki cikakke. Idan yayi niyyar kyakkyawan aiki sannan ya aikata wannan kyakkyawan aiki, to Allah zai rubutashi a matsayin kyakkyawan aiki guda goma har ya rubuntashi zuwa dari shida har zuwa ga ninkin-baninkin abin da Allah ne kawai ya san yawansa. Idan mutum yayi niyyar aikata mummuna sai kuma bai aikata mummunan ba, to Allah zai rubuta wannan rashin aikata mummunan a matsayin kyakkyawan aikine. Idan mutum yayi niyyar aikata mummuna kuma ya aikata, to Allah zai rubuta wannan mummuna a matsayin mummuna guda daya.

Idan mutum ya bada sadaka Allah yana ninka ladan har ya zuwa dari bakwai har ya zuwa ladan da shi kadai yasani. Akwai ayyukan da Allah ne kawai yasan yawan ladansu, kamar Azumi

WANDA YA GABATAR: DR. BASHEER ALIYU OMAR

4 responses

  1. To yan uwa muji tsoron Allah mu yawaita istigfari domin Allah yana amsa bukatar bawan sa ko wace irice Allah yasa mu dace ameen.

  2. Allah Ya kara Daukakah sunnah

  3. Assalamu Alaikum
    Gaskiya na yaba da irin kokarin da kukeyi na yada ilimin addinin musulunci a duniya baki, da fatar za’a kara kiyayewa da irin abubuwanda ake watsawa. Allah ya kara taimakawa ya bada ikon dorewa. Muna godiya sosai

    1. Mun gode Allah ya saka da alkhairi.

Ka bar sakonka a nan