Fitintinun da suke faruwa a garuruwan musulmi a yau

Ya bude hudubar tasa ne da yabo ga Allah da kuma salati da sallama ga Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi.
Sannan ya yi wasici da jin tsoron Allah madaukakin sarki.
Ya kusa cikin hudubar tasa yana mai Magana dangane da fitintinun da suke faruwa a garuruwan musulmi a yau.
Yana mai cewa fitintinu a yau sun kewaye musulmi a garuruwansu ta ko ina, wadda musibar da tafi ko wacce girma da cutarwa a cikin musulmi a yau it ace: musibar sabani da rarrabuwar kai, da kuma yaduwar kiyayya da kin jinin juna kuma duk sabo da kawar rayuwar duniya, wanda basu farga ba har wannan sharri ya zo ya mamayesu ya fantsama a cikinsu, cutarwa ta afkawa bayin Allah tayi kicinkicin a garuruwansu, ya gusar da aminci da kwanciyar hankalin da su ke ciki, masifa ta afkawa dukiya da rayuka, fitintinun da da suka haifar da asarar rayuka da keta mutumci, wanda hakan bai gushe da sub a har sai da takai suna suna nuna juna da amakamai, wanda sakamakon haka ne fadin Annabi ya fada masu, inda yak e cewa: (kada ku zama kafirai bayana har ya zama sashenku na kashe sahi).
Daga nan sai ya yi bayani dangane da mafita daga wannan musiba, yana mai cewa: mafita daga cikin wannan mawuyacin halin da musulmi suka fada yana cikin, komawa ga yin riko da tuwasun addininmu na muslumci mai tsarki, hakan shi ne abin da zai lamince mana aminci, ya bamu kariya daga wadannan fitintinu da sharruka da hadurori da musulmi ke ciki, kamar yadda Allay ace: lallai wadanda su ke sabawa umarnin Annabi su ji tsoron kada wata fitina ta same su ko kuma wata azaba ma radadi ta same su).
Ya ce: tsayuwa kan kadaita Allah ta’ala da kuama cikakkaen imani da shi, da yin aiki da koyarwar shari’a it ace babbar hanyar fita daga cikin wannan masifa da fitintinu, manzon Allah yana cewa: (ka kiyaye Allah sai Allah ya kiyayeka).
Yana mai cewa: hakika yana daga cikin manyan abubuwan da ya wajaba mu kiyaye su mu yi riko dasu, don katange kawukanmu daga fadawa cikin fitintinu, shi ne: karfaf dankon ‘yanuwantaka ta imani a tsakaninmu, kuma abin da yafi komai karfafa ‘yan uwantakar imani shi ne kaunar juna don Allah, da sanin hakkoki, talaka yasan hakkin shugaba, shugaba yasan hakkin wanda yake mulka (talakansa), wanda in har aka kiyaye wadannan bangarorin to aminci kam zai game kowa da komai, in kuwa har akayi shakulatun bangaro dasu to tabbas babu abin da zai mamaye al’uma in ba sharri , da masifa da fitina ba.
Sannan yay i nunu da cewa wajibi ne shugaba a ko ina ya zanto mai amana mai tsayar da adalci ga talakawansa, yana mai jin tsoron Allah a cikinsu, domin da tsayuwar adalci ne kadai mutane zasu sami zaman lafiya, maia mulki da wanda ake mulka, zalunci kuwa babu abin da yake haifarwa sai yaduwar sharri da barna da kin juna da hassada da kyashi.
Yana maia buguwa shuwagabanni misali da sayidina Umar da khattab, da irin yadda ya gudanar da mulkinsa da adalci, wanda sakamakon haka alherai suka yawaita aminci ya game ko’ina.
Sannan ya kirayi mutane da su ringa biyayya ga jagororinsu matukar basu uamarce su da kafirci ko sabon Allah, nesanta kansu da fito na fito da hukuma, da cewa in zasu yi masu nasiha to zanto a cikin sirri daga su sai su, ba a fili ko kan minbari ba.
Sannan ya rufe da umarni da yin salati ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, da kuma addu’oin samun zaman lafiya ga garuruwan musulmi, musamman wadanda ke cikin yake-yake, da tarzoma a yau.

WANDA YA GABATAR: ASSHEIKH HUSAIN ALUSSHAIKH

2 responses

  1. ALLAH YABIYA

  2. Sakallahu khairan Allah yataimakemu ameen

Ka bar sakonka a nan