ILMI AMANA NE.

Wannar huduba tazo daidai lokacin da da yawa cikin daliban manyan makarantu na gaba da sakandare suke rubuta jarrabawa, wassu kuma suna shirin farawa a ‘yan kwanaki kadan masu zuwa, musamman daliban Jami’a Mallakar jihar Gombe wanda suke shirye-shiryen farawa.

Malam yayi amfani da wannar dama yayi kira da babbar murya ga dalibai su dage matuka wajen karatu, da kuma nacewa da addu’a. ya kuma tsawatar kan harkar magudin jarrabawa yana me bayyana munin hakan da haramcinsa a shari’a.
Hudubar ta kunshi muhimman abububuwa da dukkan musulmi zai so ya sauraresu ya kuma yi amfani dasu, musamman su dalibai masu shirin rubuta jarrabawa.

@Muhimman darussa da hudubar ta kunsa sun hada da:

• Musulunci yana horon musulmi da ya zamto mai kololuwar himma cikin dukkan abun da yasa a gaba.

• Anaso Musulmi ya zamto mai kekkyawar manufa a rayuwa cikin dukkan abinda zaiyi.

• Ilmi na iya zamowa rabauta ga mutum duniya da lahira, a wani bangaren kuma yana iya zamowa halaka a duniya da lahira.

• Za’a tambayi dan adam yanda yayi mu’amala da ilminsa saboda amana ce.

• Game da sha’anin rokon ubangiji, kowanne lokaci anaso mutum ya rika rokon abu mafi kololuwa, saboda haka ne ma manzon Allah yace idan zaku roki Allah Aljanna to ku roke shi firdaus (madaukakiya).

@ Anaso dalibi mai rubuta jarrabawa ya kula matuka da wadannan abubuwa da za’a lissafo:

– riko da sababi ma’ana dukkan wani abunda zaisa ya samu sakamako mai kyau da shari’a ta yarda dashi.
– Addu’a da neman taimakon Allah da kuma sanin cewa Allah ne kawai me saukake al’amari komin wahalarsa.
– sanin muhimmancin lokaci da tsara shi.

– sanin dokokin jarrabawa.

– haramun ne sata ko magudi ta kowanne hali lokacin jarrabawa. Kuma duk wanda yayi ha’inci baya cikin al’ummar Manzon Allah s.a.w

– duk wanda ya karbi sahada ( certificate) alhali gishshu yayi, to matukar yana karban albashi da wannan haram yake ci.

– siffa ta satar jarrabawa ba dabi’ar nusulmi bane kuma bata sunan musulunci ne.

WANDA YA GABATAR: DR. RASHEED ABDULGHANIY

3 responses

  1. allah yasa mugane ya kuma bamu damar daxatasa mubauta masa daidai yan da yanda yace abauta masa

  2. Karin bayani

  3. Abubakar Khalid | Reply

    Allaah yasakawa Mallam da alkhairinsa yakumaa bada ikon tunatarwa a kodayaushe amin. Kuma akan masu bata sunan Annabi(SAW) misali wasu suce MOHAMMEeD ko MUHAMMED. Zakaji suna cewa wai da Turancine, amma Musilmin dake zuwa Israel suna cewa wajen bada SUNA idan kabada MUHAMMAD. Bazasu taba RUBUTASHIBA kodai kacanza inanufin kasa MOHAMMED ko kuma ka RUBUTA da kanka. Muna neman karin bayani akan hakan shin zamu iyayin yanda sukeso ko A’A??? BissaAllaah yasakawa Mallam da alkhairinsa yakumaa bada ikon tunatarwa a kodayaushe amin. Kuma akan masu bata sunan Annabi(SAW) misali wasu suce MOHAMMEeD ko MUHAMMED. Zakaji suna cewa wai da Turancine, amma Musilmin dake zuwa Israel suna cewa wajen bada SUNA idan kabada MUHAMMAD. Bazasu taba RUBUTASHIBA kodai kacanza inanufin kasa MOHAMMED ko kuma ka RUBUTA da kanka. Muna neman karin bayani akan hakan shin zamu iyayin yanda sukeso ko A’A??? BissaAllaah yasakawa Mallam da alkhairinsa yakumaa bada ikon tunatarwa a kodayaushe amin. Kuma akan masu bata sunan Annabi(SAW) misali wasu suce MOHAMMEeD ko MUHAMMED. Zakaji suna cewa wai da Turancine, amma Musilmin dake zuwa Israel suna cewa wajen bada SUNA idan kabada MUHAMMAD. Bazasu taba RUBUTASHIBA kodai kacanza inanufin kasa MOHAMMED ko kuma ka RUBUTA da kanka. Muna neman karin bayani akan hakan shin zamu iyayin yanda sukeso ko A’A??? BissaAllaah yasakawa Mallam da alkhairinsa yakumaa bada ikon tunatarwa a kodayaushe amin. Kuma akan masu bata sunan Annabi(SAW) misali wasu suce MOHAMMEeD ko MUHAMMED. Zakaji suna cewa wai da Turancine, amma Musilmin dake zuwa Israel suna cewa wajen bada SUNA idan kabada MUHAMMAD. Bazasu taba RUBUTASHIBA kodai kacanza inanufin kasa MOHAMMED ko kuma ka RUBUTA da kanka. Muna neman karin bayani akan hakan shin zamu iyayin yanda sukeso ko A’A??? Bissalam.

Ka bar sakonka a nan